Isa ga babban shafi

Shugaba Tinubu ya ruguza Najeriya, in ji Babacir Lawal

Najeriya – Tsohon Sakataren gwamnatin Najeriya, Babacir David Lawal ya bayyana cewar kasar ta ruguje a karkashin gwamnatin Bola Tinubu saboda halin da ta samu kan ta a yau.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Tinubu © Nigeria Presidency
Talla

Lawal yace matsalolin da suka kai ga kasar shiga irin wannan mummunar yanayi sun fara ne tun ranar da shugaban kasa Tinubu ya sanar da janye tallafin man fetur, ba tare da tattaunawa da majalisar ministocin sa ba a kan illar dake iya biyo baya ba.

Tsohon Sakataren yace wannan mataki ya sanya harkokin sufuri sun yi tashin goran zabbi da kuma shafar kusan kowanne fanni na rayuwa ga talakawa da ma masu hanu da shuni.

Lawal yace a lokacin yana sayen mota guda na abincin dabbobi a kan kudi naira dubu 270, amma da cire tallafin sai farashin ya yi tashin da ba zai iya saye ba, saboda yadda kudin sufurin da yake biya kawai ya kai kusan naira miliyan guda.

Tsohon jami'in ya shaidawa Jaridar Daily Trust cewar a makon jiya ya sayi motocin aikin noma guda 3 a Kano, amma kudin daukar su kawai ya kai naira miliyan 3, saboda irin wannan yanayi da jama'a suka samu kan su a Najeriya.

Babacir wanda ke cikin 'yayan jam'iyyar APC da suka bijire mata saboda tsayar da Bola Tinubu da Kashim Shettima da suka fito daga addini guda, yace 'yan Najeriya na cikin mawuyacin hali a karkashin wannan gwamnatin dake cika shekara guda a karagar mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.