Isa ga babban shafi
Birtaniya

Wani mutum ya kashe soja a kasar Birtaniya

Jiya laraba aka kashe wani mutum da ake ganin sojan kasar Britaniya ne, a kusa da wani barikin sojan da ke birnin London, lamarin da Firaminista, David Cameron ya ce, ya yi kama da harin ta’addanci.

Mutumin da ake zargi da kashe sojan Birtaniya dauke da wukar da ya yi kisan
Mutumin da ake zargi da kashe sojan Birtaniya dauke da wukar da ya yi kisan Reuters
Talla

Wani hoton Bidiyon da aka gani, ya nuna daya daga cikin maharan na dauke da wukake jina jina, yana kallon na’urar daukar hoto yana cewa mun rantse da Allah, ba za mu daina fada da ku ba.

Mutumin, da bakar fata ne ya kuma yi wasu kalaman da suka shafi siyasa ga mutanen da ke wucewa.

Sai dai ‘yan sanda sun harbi, tare da raunata mutanen biyun da suka kashe sojan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.