Mutane 16 sun kone kurmus a Nijar
A Jamhuriyar Nijar wata karamar motar fasakwarin man feutr ta yi sanadiyar mutuwar mutane 17 sakamakon harbin bidinga da wani jami’in kwastam ya yi a karamar hukumar Tsauni dake cikin gudumar Matamaye yankin Zinder kan iyaka da Tarrayar Najeriya a yayinda wasu da dama suka jikata.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Al'amarin ya faru ne a lokacin da Jam'ian Kwastam suka yi kokarin dakatar da motar yan fasa kwabrin dake dauke da buburutan man fetur ,bayan direban ya ki tsayawa ne, daya daga cikin jami'an kwastam ya bude wuta da bidinga,inda nan take ta kama da wuta ta kuma fada a cikin wani gida mai cinkoson jama'a a garin na Tsauni.
Nan take Direban da mutane 16 ne suka kone kurmus.
Yanzu haka mahakunta sun sanar da soma gudanar da binciken gano gaskiyar dalilin faruwar hadarin.
A baya dai an sha zargin Jami’an kwastam da harbe mutanen har lahira da sunan yaki da fasakwabri a kasar ta Jamhuriyar Nijar dake samu kusan daukacin kudaden shigarta daga haraji.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu