Jamhuriyyar Nijar zata yi bikin cika shekaru 58
Jamhuriyar Nijar zata gudanar da shagulgulan cikarta shekaru 58 da zamanta Jamhuriya ranar 18 ga watan Disamba mai zuwa, inda a wannan shekara jihar Agadez zata zama mai daukar nauyin shagulgulan, kamar yadda aka zagaya dasu wasu jahohin kasar a baya.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Malam Mahamed Abdulkadir da ake kira Maidalili, dan kungiyar farar hula a kasar, ya kuma shaidawa Sashin Hausa na RFI cewa yayin bikin mutanen Agadez masu sama da shekaru 60 basu taba gani, da ya kunshi nadin sarauta da za’a yiwa Mai Martaba Sarkin Azbin Ibrahim Ummaru, sai kuma wankan sarautar da za’a yi masa.
A cewar Abdulkadir akwai kuma shirin atasaye na gudun sassarfa da za’ayi wanda ya kunshe ‘yan kasashen ketare, domin karfafa zaman lafiya da kuma hadin kai, tsakanin al’ummar Jamhuriyyar Nijar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu