Bakonmu a Yau
Kungiyar Alkalan Jamhuriyar Nijar kan binciken almundahana a cinikin makamai
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:29
Kungiyar Alkalai a jamhuriyar Nijar, ta zargi gwamnatin kasar da kokarin yin rufa-rufa a game da sakamakon binciken da ma’aikatar tsaron kasar ta yi, dangane da cinikin makamai da bilyoyin kudade.Kungiyar ta zargi gwamnati da neman yin shishigi a lamurran da suka shafi shari’a, bayan da ta bukaci wadanda aka bai wa kwangila a ma’aikatar tsaron su gaggauta aiwatar da kwangilar ko kuma a gurfanar da su a gaban kotuna.Mai Shari’a Nouhou Aboubacar, shi ne shugaban kungiyar alkalai SAMAN, ya yi man karin bayani a zantawarmu.