Isa ga babban shafi
Nijar - Ta'addanci

Nijar: 'Yan Tillaberi fiye da dubu 11 sun koma kauyukansu bayan hijirar tilas

Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun maida mutane fiye da dubu 11 zuwa kauyukansu dake yankin Tillaberi a yammacin kasar, bayan da hare-haren ‘yan ta’adda ya tilasata musu tserewa a watannin baya bayan nan.

Wani sansanin 'yan gudun hijira a Jamhuriyar Nijar.
Wani sansanin 'yan gudun hijira a Jamhuriyar Nijar. © picture-alliance/dpa
Talla

Yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na AFP a yau, gwamnan yankin na Tillaberi Tijjani Ibrahim Kachalla, ya ce ‘yan gudun hijirar dubu 11 da 200 aka  maida su gida, yayin da ya rage kimanin dubu 1000 wadanda su ma wani lokaci a yau ake sa ran komawar ta su gida.

Ranar Juma’ar da ta gabata, gwamna Tijjani Kachalla ya kaddamar da shirin maida dubban ‘yan gudun hijirar zuwa garuruwansu, tare da rakiyar jami’an tsaro.

A farkon makon da ya kare, Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane fiye dubu 11 sun tsere daga kauyukansu a yankin Tillaberi sakamakon fama da hare-haren ‘yan ta’adda.

A wani rahoton na dabam, Majalisar Dinkin Duniyar ta ce zuwa karshen watan Janairun wannan shekara, hare-haren ‘yan ta’adda masu biyayya da kungiyoyin IS da Al Qaeda sun raba mutane kimanin dubu 100a da kauyukansu, katsewa wasu kimanin dubu 30 samun kulawar lafiya da kuma rufe makarantu kimanin 300, a yankin na Tillaberi da yayi iyaka da kasashen Burkina Faso da Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.