Isa ga babban shafi
NIJAR-MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana shirin aiki da hukumomin Nijar

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana aniyar ta na aiki tare da hukumomin Jamhuriyar Nijar wajen samar da zaman lafiya da kuma cigaban jama’ar kasar.

Shugaban Nijar Bazoum Mohammed tare da Jakadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman a yankin Sahel Annadif Mahamat Saleh
Shugaban Nijar Bazoum Mohammed tare da Jakadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman a yankin Sahel Annadif Mahamat Saleh © Niger Presidency
Talla

Jakadan Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya na musamman dake kula da yankin Afirka ta Yamma da Yankin Sahel Mahamat Saleh Annadif ya bayyana haka lokacin da ya ziyarci shugaban kasa Bazoum Mohammed a birnin Yammai.

Annadif yace suna sane da kalubalen tsaron da ya addabi Nijar da wasu kasashen dake yankin kuma a shirye suke taimaka mata a koda yaushe domin tinkarar sa.

Shugaba Bazoum Mohammed tare da Annadif Mahamat Saleh Jakadan MDD na musamman akan Yankin Sahel
Shugaba Bazoum Mohammed tare da Annadif Mahamat Saleh Jakadan MDD na musamman akan Yankin Sahel © Niger Presidency

Jakadan yace Majalisar ta taimakawa Jamhuriyar Nijar wajen samun nasarar zaben shugaban kasar da ya gabata wanda ya tabbatar da mika mulki daga zababben shugaba farar hula zuwa wani zababben shugaban, wato daga tsohon shugaban kasa Mahamadou Issofou zuwa sabon shugaban kasa Bazoum Mohammed.

Annadif yace sun tattauna da shugaban kasar Nijar akan rawar da kasar zata cigaba da takawa domin zama abin misali ga sauran kasashen dake yankin.

Yanzu haka Jamhuriyar Nijar na daga cikin kasashen duniya dake rike da kujeru a kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.