Birtaniya ta gayyaci Bazoum taron bunkasa ilimi
Gwamnatin Birtaniya ta gayyaci shugaban Jamhuriyar Bazoum Mohammed domin halartar taro akan harkokin bada ilimi da kasar zata shirya.
Wallafawa ranar:
Ministan Birtaniya dake kula da harkokin Afirka James Duddridge ya mika takardar gayyatar ga shugaba Bazoum lokacin da ya ziyarce shi a fadar sa dake birnin Yammai.
Duddridge ya taya shugaban kasar murnar nasarar zaben da aka samu a kasar da kuma mika mulki ba tare da samun wata matsala ba, yayin da suka tattauna kan batutuwa da dama da suka hada da matsalar tsaro a yankin Sahel da tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.
Bayan ganawar ministan ya bayyana farin cikin sa da amsa gayyatar shiga taron da zai gudana a Birtaniya da shugaba Bazoum yayi musamman saboda yadda gwamnatin sa ke fifita bangaren bada ilimi.
Shugaba Bazoum Mohammed ya sanya batu inganta ilimin mata a cikin manufofin gwamnatin sa domin ganin mata sun daina barin karatu domin yin aure ko kuma yin wasu sana’oi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu