Isa ga babban shafi
GASAR-OLYMPICS

Bazoum yayi ban kwana da tawagar 'Yan wasan Olympics

Shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed ya bukaci tawagar 'Yan wasan kasar da zasu wakilce ta a gasar Olympics da zai gudana a birnin Tokyo karo na 32 da su jajirce wajen daga darajar Nijar.

Shugaba Bazoum Mohammed dauke da tutar Nijar
Shugaba Bazoum Mohammed dauke da tutar Nijar © Niger Presidency
Talla

Yayin da yake jawabin ban kwana da tawagar kafin barin Nijar zuwa Japan, shugaban ya bayyana cikakken goyan bayan sa da na jama’ar kasar ga tawagar Yan was an inda ya musu fatar tafiya lafiya da kuma samun nasara.

Daga cikin tawagar Yan wasan akwai Abdoul Razak Alfaga, zakaran duniya da Afirka a wasan kokawar taekwondo kuma mai rike da kambin azurfa a gasar Olympics.

Jagoran Yan wasan Nijar Abdoul Razaq Alfaga yana karbar tutar kasar
Jagoran Yan wasan Nijar Abdoul Razaq Alfaga yana karbar tutar kasar © Niger Presidency

Sauran sun hada da Yan tsere guda 2 da Yan wasan ninkaya guda 2 da ‘dan wasan judo guda.

Bazoum ya shaidawa Alfaga cewar suna sarai da shi da kuma sauran ‘yan wasan wajen samun nasara, duk da yake basu da yawa kamar sauran kasashen duniya.

Shugaban kasar yace zasu ci gaba da yiwa ‘yan wasan addu‘ar fatan alheri domin ganin sun isa Tokyo lafiya sun kuma koma gida lafiya.

Shugaba Bazoum Mohammed tare da tawagar Yan wasan da zasu wakilci kasar a Tokyo
Shugaba Bazoum Mohammed tare da tawagar Yan wasan da zasu wakilci kasar a Tokyo © Niger Presidency

A ranar 23 ake saran bude gasar Olympics a birnin Tokyo wanda za’a kamala shi ranar 8 ga watan Agusta.

Gasar karo na 32 ta fuskanci matsaloli da dama sakamakon annobar korona, inda aka fasa gabatar da ita a shekarar da ta gabata, yayin da a makon jiya kuma aka sanar da haramtawa ‘yan kallo saboda sake dawowar annobar a wasu kasashe ciki harda Japan mai daukar nauyin kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.