Mutane 35 suka mutu sanadiyyar ambaliya a jamhuriyar Nijar
Ruwan sama dai-dai da bakin kwariya da aka soma tun a farkon watan Yuni a Jamhuriyar Nijar sun hadasa mutuwar mutane 35 tareda tilastawa kusan dubu 26.500 barin matsugunin su.
Wallafawa ranar:
A wani rahoto na baya-bayan nan daga hukumar kare jama’a ta Jamhuriyar Nijar da kamfanin dillanci labaren Faransa ya samu a jiya asabar mutane 20 ne suka mutu bayan ruftawar gidajen su.
Yankunan da abin ya fi muni sun hada da Maradi inda aka samu mutuwar mutane 10,Agadez dake arewacin kasar mutane 10 suka mutu a yankin sai babban birnin kasar Yameh inda aka samu mutuwar mutane 8.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu