Isa ga babban shafi
Nijar-Yancin kai

Nijar na bikin Tunawa da ranar samun yancin-kai

A yau Talata 3 ga watan Agusta Jamhuriyar Nijar ke gudanar da bukukuwan cika shekaru 61 da samun ‘yancin kai daga Faransa.

 Bazoum Mohammed shugaban Nijar.
Bazoum Mohammed shugaban Nijar. © Niger Presidency
Talla

A jawabinsa da ya gabatar wa al’ummar kasar jajibirin wannan rana, shugaba Mohamed Bazoum ya tsokaci ne a game da matsalar tsaro sakamakon hare-haren ‘yan ta’adda a yankuna da dama na kasar, da batun yaki da rashawa sai kuma kokarin da mahukunta ke yi don shawo kan annobar covid-19.

A game da matsalar tsaro, shugaba Bazoum ya jinjina wa jami’an tsaron kasar sakamakon namjin kokari wajen tunkarar ayyykan ta’addancin kungiyar EIGS da ke da’awar jihadi a yankin Sahara, kungiyar da magoya bayanta suka kashe fararen hula da dama a  garuruwan Bakorat, Intazayène, Tchomabangou, Zaroumdarey, Deye Koukou, Wiyé, Zibane da dai sauransu daga bara zuwa bana.

A game da yaki da rashawa kuwa, shugaban na jamhuriyar Nijar ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da daukar matakan ba sani ba sabo don kawo karshen wannan dabi’a, ciki har da satar jarabawa a makarantu ko kuma lokacin dibar ma’aikata.

Bazoum ya ce don kawo karshen irin wadannan matsaloli ne ya shirya ganawa da kungiyoyin kwadago da na fararen hula don jin shawarwarinsu da kuma yadda za a tunkari matsalolin ta hadin gwiwa.

Shugaba Mohamed Bazoum ya yi kira ga ‘yan kasar da su amince a yi masu allurar rigakafin kariya daga cutar covid-19, musamman lura da yadda aka fara samun nau’in cutar da ake kira Delta.

A bana, kamar dai kowace shekara, ana amfani da zagayowar ranar ta ‘yancin-kai don gudanar da dashen itatuwa da ke matsayin yunkurin hana gurgusowar hamada a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.