Wasu 'yan Nijar sun mutu a cikin dajin hamadar Tunisia
An gano gawarwakin mutane 6 mata biyu da kuma kananan yara 4 da aka bayyana cewa ‘yan Nijar ne da suka mutu sakamakon kishirwa a cikin dajin hamadar kasar Tunisia.
Wallafawa ranar:
Hukumar de ke kula da bakin haure ta Majalisar Dinkin duniya OIM, ta ce kusan mutane dubu 6 suka mutu a tekun Meditareniya a kokarin su na ketarawa Turai cikin shekaru 5, duk da cewa an samu ragowar adadin mutanen da ke rasa rayukan su a ‘yan tsakanin nan.Garin Agadez ya kasance wata hanya da bakin ke anfani da ita don cimma burin su.
Tsawon shekaru ,hukumomin Nijar na yakar kungiyoyin dake daukar nauyin tsallakawa da irin wadanan mutane,kazalika kasashe irin su Libya,Mauritania da Tunisia a duk kullum sojojin wadanan kasashe na gano gawarwakin mutane cikin dajin hamadar dake kokarin tsallakawa don neman mafaka ta gari a yankin Turai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu