Isa ga babban shafi
Nijar-Yunwa

Mutane dubu 600 na fuskantar bala'in yunwa a Nijar

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa, yankin Tillaberi na yammacin Jamhuriyar Nijar na fuskantar babbar matsalar abinci, inda kusan mutane dubu 600 ke fama da matsalar karancin abinci.

Wata mata tare da yaranta a kauyen Tamou dake wajen birnin Yamai a Jamhuriyar Nijar.
Wata mata tare da yaranta a kauyen Tamou dake wajen birnin Yamai a Jamhuriyar Nijar. ASSOCIATED PRESS - TAGAZA DJIBO
Talla

Ofishin Kula da Ayyukan Jin-Kai na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa, rashin tsaro da hare-haren da ake zargin wasu kungiyoyin masu dauke da makamai da ke kai hari ga manoma da fararen hula za su haifar da mummunan sakamako a wannan shekarar kan halin rashin abinci.

Yankin na Tillaberi da ya kai girman Koriya ta Kudu ko Hungary, na da iyaka da kasashen Burkina Faso da Mali da Benin.

Majalisar Dinkin Duniya ta kuma yi gargadin halin da ake ciki a sashin Banibangou zuwa arewa maso gabashin Tillaberi, inda ake sa ran sama da mutane dubu 79 za su su fuskanci tsananin yunwa.

Tsakanin watan Yuni da Agustan shekarar da muke ciki, wani gungun 'yan bindiga ya kashe manoma da dama a Banibangou a cikin gonakinsu, wanda hakan ya tilasta wa jama'a yin watsi da gonakinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.