Isa ga babban shafi
Nijar

Kotu ta ba da izinin yin zanga-zangar adawa da sojojin kasashen waje dake Nijar

Wata kotu a Jamhuriyar Nijar ta ba da damar gudanar da zanga-zangar da kungiyoyin farar hula suka shirya gudanarwa a ranar Lahadi domin neman rufe sansanonin sojojin kasashen waje da ke kasar, wadda ta shafe shekaru da dama tana fuskantar munanan hare-haren 'yan ta’adda masu ikirarin Jihadi.

Wani sojan Faransa yayin kula da yankin Gourma garin Ndaki, dake kasar Mali, ranar 27 ga Yuli, 2.
Wani sojan Faransa yayin kula da yankin Gourma garin Ndaki, dake kasar Mali, ranar 27 ga Yuli, 2. © Benoit Tessier/Reuters
Talla

Daya daga cikin wadanda suka shirya zanga-zangar Maikoul Zodi, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa kotu ta yanke hukuncin ne a ranar Juma’a, inda kuma ta bukaci 'yan sanda su kula da gudanar zanga-zangar cikin lumana.

A cewar Zodi sun bukaci yin zanga-zangar kan neman ficewar dukkan sansanonin sojojin kasashen waje musamman na Faransa, saboda yadda suka shafe shekaru takwas suna Nijar ba tare da kawo karshen matsalolin tsaron da suke fuskanta ba.

A karshen watan Nuwamba, ayarin motocin sojojin Faransa dake kan hanyarsu ta zuwa kasar Mali suka fuskanci turjiya a garin Tera dake jamhuriyar Nijar bayan shafe sama da mako guda ana gudanar da zanga-zangar rashin amincewa da jerin gwanon motocinsu a Burkina Faso.

Ayarin motocin sojin na Faransa da suka sauka a kasar Ivory Coast, sun fara tsallakawa ne Burkina Faso, kafin daga bisani su shiga Nijar a kan hanyarsu ta zuwa tsakiyar Mali, inda suka fuskanci turjiyar masu zanga-zanga kimanin dubu 1, a garin Tera dake yammacin kasar ta Nijar, lamarin da yayi sanadin mutuwar mutane uku tare da jikkatar wasu 18 a ranar Asabar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.