Isa ga babban shafi

'Yan ta'adda sun yi wa sojojin Nijar kwanton bauna a tsakiyar hamada

Sojojin Jamhuriyar Nijar 2 suka mutu, yayin da wasu guda 4 suka samu raunuka lokacin da Yan ta’adad suka kai musu hari a tsakiyar hamada kusa da wani wuri da ake kira Plague 50.

Sojojin Nijar yayin sintiri a iyakar kasar da Najeriya.
Sojojin Nijar yayin sintiri a iyakar kasar da Najeriya. REUTERS/Luc Gnago
Talla

Rahotanni sun ce sojojin sun dauki hutu ne inda suka dauki motar haya zuwa Agadez lokacin da aka samu hadarin da Yan bindiga suka bude musu wuta.

Jamhuriyar Nijar na cigaba da fuskantar matsalar Yan ta’adda dake kai hare hare akan fararen hula da jami’an tsaro.

A farkon watan Afrilu, rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce hare haren ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi a wasu yankuna na gabashi da tsakiyar Mali sun tsananta matuka ta yadda ako wanne lokaci suke haddasa asarar rayukan gwamman fararen hular da basu ji ba basu gani ba, kari kan jami'an tsaro da 'yan sa kai da ke mutuwa a kowacce rana.

Rundunar ta ce matsalar tsaro a iyakoki  3 na tsakanin Mali, Nijar da Burkina Faso ta ta’azzara, musamman a  yankunan Tessit, Talataye, Ansongo da Menaka a cewar wata sanarwa da ta fitar a Alhamis din makon nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.