Isa ga babban shafi

'Yan ta'adda sun kashe 'yan sandan Nijar

Wasu 'yan ta’adda a iyakar Burkina Faso sun kashe ‘Yan Sandan Jamhuriyar Nijar guda 7, yayin da wasu 16 suka samu raunuka lokacin da suka kai musu hari a matsuguninsu.

Wasu Jami'an 'yan sandan jamhuriyar Nijar
Wasu Jami'an 'yan sandan jamhuriyar Nijar © RFI Hausa
Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito cewar tawagar 'yan bindigar dauke da muggan makamai sun kai harin ne a tashar 'Yan Sandan da ke Petelkole.

Wani jami’in hukumar yankin ya tabbatar da adadin ‘Yan sandan da aka kashe da kuma wadanda suka jikkata, yayin da zuwa wannan lokaci gwamnatin Nijar bata ce komai dangane da harin.

Ana kyautata zaton maharan na daga cikin kungiyoyin Yan ta’addan dake alaka da kungiyar IS, kuma sun yi nasarar kwace motoci guda 3 lokacin harin da kuma lalata wasu da dama.

Rahotanni sun ce an kai wannan harin ne a Yankin Tera dake Jihar Tillaberi wadda ke da iyaka da Burkina Faso da kuma Mali, inda ake samun yawan hare haren Yan ta’adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.