Isa ga babban shafi

Shugaban Nijar ya kai ziyara yankin Diffa

Shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed yanzu haka yana ziyarar aiki a Jihar Diffa shekara guda bayan mayar da Yan gudun hijirar Boko Haram da rikici ya raba da muhallin su gida.

Shugaban Nijar Bazoum Mohamed a yayin ziyarar da ya kai jihar Diffa.
Shugaban Nijar Bazoum Mohamed a yayin ziyarar da ya kai jihar Diffa. © Niger's presidency
Talla

Ziyarar ta shugaban na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin Nijar tare da takwarorin su na kasashen Tafkin Chadi ke ci gaba da samun galaba wajen murkushe mayakan dake kai hare hare a yankin.

Rahotanni sun ce tsakanin ranar 28 ga watan Maris na wannan shekarar zuwa 4 ga watan Yuni, rundunar hadin kan tayi nasarar kashe mayakan Boko Haram da ISWAP akalla 800, tare da kwace motoci 44 da Babura 22 da kuma tarin makamai manya da kanana

 Shugaban ya gana da kwamandodin tsaro da masu aikin agaji da 'yan gudun hijirar da suka koma gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.