Tawagar Gwamnatin Nijar ta ziyarci garin Tamou
Ministan harakokin cikin gida na Jamhuriyar Nijar Hama Adamou Souley, ya shugabanci babbar tawagar da ta kunshi hafsan hafsoshin soji, da gwamnan Tillabéri, da babban kwamandan tsaron kasa, suka ziyarci Tamou a safiyar yau asabar don duba halin da ake ciki, su kuma gane gaskiyar lamarin, biyo bayan harin ta'addancin da aka kai mahakar zinari da Ofishin ‘yan sanda na Tamou a ranar 24 ga Oktoba, 2022, wanda ya yi sanadin mutuwar ‘yan sanda biyu .
Wallafawa ranar:
Ministan cikin gida ya sheidawa manema labarai cewa za a gudanar da bincike don tabbatar da matsayin wadanda suka jikkata domin bambance masu aikin ta'addanci da wadanda ba su ba.
Yawancin wuraren hakar gwal a wannan yanki 'yan ta'adda ne ke yawan zuwa, wadanda sukan yi amfani da masu aikin hakar zinare a matsayin mafaka.
Gwamnati dai ta dade tana ba wa kananan hukumomin umarnin gudanar da gangamin wayar da kan jama’a domin gujewa wadannan wuraren boye da kuma daina duk wani nau’i na hadin gwiwa da yan ta’adda.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu