Isa ga babban shafi

Tsaro: Wani kamfanin hakar ma'adinan Faransa a Nijar ya kwashe ma'aikatansa

Kamfanin hakar Uranium na Faransa Orano ya ce ya kwashe ma'aikatan sa daga arewacin Nijar bayan gargadi game da wata barazana a yankin da ke fama da masu tayar da kayar baya.

Matsalar tsaro ta tilastawa kamfanin kwashe ma'aikatan nasa daga arewacin kasar
Matsalar tsaro ta tilastawa kamfanin kwashe ma'aikatan nasa daga arewacin kasar AFP - ERIC PIERMONT
Talla

A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar ta ce a yammacin ranar Alhamis aka aike wa kamfanin sako kan wani taron tsaro a wani kauye da ke tsakiyar kan iyakar Mali da garin Arlit da ake hakar ma'adinai.

Ma'aikatan Orano 'yan kasashen waje da wasu ma'aikatan sa da ke aiki na wucin gadi na zaune a wani katafaren gida da ke Akokan kusa da Arlit "an kwashe su zuwa Yamai," babban birnin Nijar, in ji sanarwar.

"Ya kamata a dawo da dukkan ma'aikatan da aka kwashe nan da 'yan kwanaki masu zuwa da zaran an tabbatar da cewa za a iya kawar da duk wani hadari da ke tunkarar su," in ji Orano.

Wata majiyar kamfanin ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa an kwashe mutane 16 da suka hada da 'yan kasashen Turai 12 da kuma mutum hudu da suka fito daga yammacin Afirka.

Orano shi ne magajin kamfanin Areva na kasar Faransa, wanda ke da muradin hakar uranium a Nijar shekaru da dama.

A shekarar 2010, wasu ma'aikata dauke da makamai sun yi garkuwa da ma'aikatan Areva bakwai da ssuka kunshi Faransawa biyar, dan Togo da kuma Madagascar a Arlit.

Daya daga cikin Faransawan da aka kama, Francoise Larribe, an sake shi bayan watanni biyar tare da ‘yan Madagascar da Togo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.