Isa ga babban shafi

Kwamandan MNJTF ya bukaci dakarunsa su kara kaimi wajen murkushe 'yan ta'adda

Kwamandan Dakarun hadin kan dake yaki da kungiyar book haram ta MNJTF, Manjo Janar Gold Chibuisi ya bukaci sojojin dake aiki a karkashinsa da su kara kaimi wajen murkushe mayakan dake dauke da makamai da zummar ganin sun kammala aikin da aka dora musu. 

Sarkin Komadougou da ke Diffa, Alhaji Kazelma Mamadou Kyari, yayin karbbar bakuncin Kwamandan dakarun hadin kan dake yaki da kungiyar book haram ta MNJTF, Manjo Janar Gold Chibuisi a fadarsa.
Sarkin Komadougou da ke Diffa, Alhaji Kazelma Mamadou Kyari, yayin karbbar bakuncin Kwamandan dakarun hadin kan dake yaki da kungiyar book haram ta MNJTF, Manjo Janar Gold Chibuisi a fadarsa. © RFI/Hausa
Talla

Janar Chibuisi ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci dakarun dake aiki a Malam-Fatori dake Jihar Yoben Najeriya da kuma Diffa dake Jamhuriyar Nijar domin kara musu kaimi akan ayyukan da suke yi. 

Kwamandan ya bukaci sojojin da su dada zagewa wajen yaki da ayyukan ta’addanci da kuma tabbatar da dawowar tabbataccen zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, yayin da ya jinjina musu akan jajircewar da suke nunawa wajen samun nasara kamar yadda duniya ta gani, musamman abinda ya shafi jarunta da mayar da hankali da kuma kwarewar da suke nunawa a cikin ayyukansu. 

Ziyarar Janar Chibuisi zuwa Malam-Fatori da Diffa na daga cikin ayyukan da yake yi na gani da ido da kuma baiwa sojojin karfin gwuiwar da suke bukata wajen ayyukansu na tsaron kasa da kuma kawar da ayyukan ta’addanci a yankin. 

Kwamandan yayi amfani da wannan damar wajen ji kai tsaye daga dakarunsa dangane da abinda ya shafi bukatunsu da kuma kayan aikin da suke bukata, yayin da ya tabbatar musu cewar rundunar MNJTF dake karkashinsa za tayi abinda ya dace wajen taimaka musu domin ganin sun samu nasara. 

Babban jami’in yada labaran rundunar ta MNJTF dake da cibiya a kasar Chadi, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi yace, Janar Chibuisi yayi amfani da damar da ya samu ta ziyarar wajen zuwa fadar Sarkin Komadougou dake Diffa, Alhaji Kazelma Mamadou Kyari inda ya gabatar da godiyarsa akan irin taimakon da suke baiwa dakarunsa. 

Sarki Kyari wanda ya yi wa dakarun addu’ar samun nasara, ya kuma jinjinawa kwamandan saboda yadda yake yawan ganawa da shugabannin yankin dake karkashin jagorancinsa. 

Ita dai wannan runduna ta MNJTF an kafa ta ne domin tabbatar da zaman lafiya da kuma tsaro a yankin Tafkin Chadi dake fama da matsalar rikicin mayakan book haram, kuma tana dauke da sojoji daga kasashen Najeriya da Nijar da Chadi da Kamaru da kuma Jamhuriyar Benin. 

Kanar Abdullahi yace rundunar ta samu gagarumar nasara wajen yaki da ta’addanci da kuma mayar da zaman lafiya a yankin, yayin da ake saran wannan ziyara ta Janar Chibuisi karawa sojojin kaimi. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.