Isa ga babban shafi

Fadar shugaban Nijar ta yi karin haske kan yunkurin juyin mulki

Fadar gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta fitar da sanarwa dangane da halin da ake ciki na fargabar yiwuwar shirin juyin mulki, inda ta tabbatar da cewa lallai an samu wasu sojoji da ke tsaron fadar shugaban kasa da suka dauki matakin da ya saba wa doka.

Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum
Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum AP - Ludovic Marin
Talla

Sanarwar ta ce gungun sojojin da suka yi wannan yunkuri ya gaza samun goyon bayan sauran takwarorinsu da ke tsaron fadar shugaban kasar ta Nijar, kuma a halin da ake ciki shugaba Bazoum Mohamed da iyalinsa na cikin koshin lafiya.

Rundunar sojin Nijar ta kara da cewar a shirye take ta dauki matakin murkushe dukkanin wadanda suke da hannu a yunkurin sabawa dokar da aka yi a baya-bayan nan, muddin ba su gaggauta tuba ba.

Da safiyar wannan Laraba ce dai aka wayi gari da matakin da jami’an tsaro suka dauka na datse hanyar da ke kai wa fadar shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohamed, a cikin wani yanayi da ake fargabar mai yiwuwa na barazanar juyin mulki ne.

Jamhuriyar Nijar da ke yammacin nahiyar Afirka na daga cikin kasashen da ke gaba wajen fuskantar matsaloli na juyin mulki, wanda ya auku sau hudu a kasar, tare da yunkurin aiwatar da wasu da dama, tun bayan da ta samu ‘yancin kai da Faransa a shekarar 1960.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.