Isa ga babban shafi

Tarayyar Turai ta dakatar da tallafin da ta ke bai wa Jamhuriyar Nijar

Kungiyar Tarayyar Turai ta ce ta dakatar da duk wani tallafi na kudi da take bai wa Nijar tare da yanke duk wata hulda a kan abin da ya shafi tsaro a tsakaninta da ita,  biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar.

Jagoran shata manufofin hulda da kasashe na Tarayyar Turai Josep Borrell.
Jagoran shata manufofin hulda da kasashe na Tarayyar Turai Josep Borrell. REUTERS - VLADISLAV CULIOMZA
Talla

Jagoran manunfofin hulda da kasashe na Tarayyar Turai Josep Borrell ne  ya  bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.

Wadandaa suka yi wannan juyin Mulki na Nijar dai sun ayyana Janar Abdourahamane Tiani a matsayin shugaban kasa a ranar Juma’a, bayan da suka wancakalal da shugaba Mohamed Bazoum.

Tarayyar Turai,  Amurka da sauran kasashen duniya sun yi kira da a saki shugaba Bazoum ba tare da gindaya wasu sharruda ba, kana a maido da Mulki dimokaradiyya a kasar.

Nijar ce kasar da ta fi samun tallafi  daga kasashen yammacin Turai,,kuam babbar abokiyar aikin Tarayyar Turai a wajen yaki da bakin haure da ke bi ta sahara zuwa nahiyar Turai.

Bugu da kari, Tarayyar Turai tana da dakaru da ke aikin bada horo a Jamhuriyar Nijar.

Kungiyar Tarayyar Turai ta wallaafa a shafinta na intanet cewa ta kasafta kudin da ya kai Yuro miliyan 503 tundaga shekarar 2021 don bunkasa sha’anin mulki da ilimi a Jamhuriyar Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.