Cape Verde na adawa da batun tura sojoji kasar Nijar
Shugaban kasar Cape Verde, José Maria Neves, ya ce kasarsa mamba ce a kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS, tana mai adawa da matakin aikewa da soja a Jamhuriyar Nijar.
Wallafawa ranar:
Duk da cewa kasar tana goyon bayan maido da Shugaba Bazoum a kan karagar mulkin kasar, amma shugaban na Cape Verde ya nuna cewa ba za a iya yin hakan ta hanyar shiga tsakani ba.
Bayan taron na Abuja,shugabannin kungiyar sun yanke shawarar yin amfani da diflomasiya kafin tunanin amfani da karfi soja domin warware wannan matsala a Nijar.
Shugaban kasar José Maria Neves, a jawabin da ya gabatarwa yan kasar a jiya Juma'a a tsibirin Fogo, ya ce "Dole ne dukkanmu mu yi aiki don maido da tsarin mulki a Nijar ta hanyar sulhu da diflomasiya.
Shugaban na Cape Verde ya kuma bayyana cewa da wuya kasarsa za ta shiga tsakani tareda da tura soji idan ECOWAS ta yanke shawarar daukar mataki. "
Shugaban kasar Cote D’Ivoire, Alassane Ouattara da dawowa daga taron Abuja, ya sanar da cewa, baya ga kasarsa, Najeriya da Benin, sun yi alkawarin hada sojoji a cikin wannan tsarin na shiga tsakani.
Shugaba Ouattara ya sanar da wata bataliya ta Cote D’Ivoire mai yawan sojoji 850 zuwa 1,100 a matsayin gudunmawar rundunar ta ECOWAS da nufin shiga tsakani a Nijar. A halin yanzu, kuma duk da barazanar, ana ci gaba da muhawara game da yiwuwar wannan shiga tare da fuskantar manyan kalubale.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu