Isa ga babban shafi

Faraminstan Nijer Mahaman Lamine Zein da ya ziyaarci Mali kan huldar tsaro da tattalin arziki

A ci gaba da kokarin hada karfi da karfe ta fannin siyasa tattalin ariziki da kuma tsaro ne shugaban Gwamnatin mulkin sojin kasar  Jamhuriyar Nijer, Ali Mahaman Lamine Zeine, a ranar laraba ya kai wata  ziyarar aiki birin  Bamako na kasar  Mali, inda ya gudanar da wata tattaunawa mai matukar  muhimmanci da tawagar a takwaransa na Mali  Choguel Maïga, kafin daga bisani ya yi wata ganawa ta musaman da   da shugaban gwamanatin  mulkin sojin kasar colonel Assimi Goïta.

Ali Mahaman Lamine Zeine, Waziri shugaban gwamnatin jamhuriyar Nijer
Ali Mahaman Lamine Zeine, Waziri shugaban gwamnatin jamhuriyar Nijer © AFP
Talla

An aganin ziyarar a matsayin ta neman mafita wajen agance radadin takunkuman da kungiyar Ecowa ko Cedeao ta kakabawa kasar ta Nijer tun bayan juyin mulkin sojin da ya kifar da zababben shugaban mulkin farar hukar kasar   Mohamed Bazoum, a ranar 26 yulin  2023.

Kasar Mali dai ta taba fuskanta takunkuman matsin tattalin arziki da ga kungiyar ta Ecowa kuma ta sha, wanda mahukumtan Nijer ke ganin akwai irin shawarwari masu amfani da zasu samu daga gareta, domin ko yi da irin dubarun da ta yi amfani da su a lokacin da kasar ta Mali ke cikin takunkuman na Ecowas

Ministocin tsaron  kasashen biyu,  su ma sun bada bahasi kan halin da ake ciki a fagen dagar yaki da yan ta’adda a cikin kasashensu.

Idan dai ba a anta ba kasashen Mali , Nijer da Burkina Faso ba da jimawa ba ne suka cimma wata yarjejeniyar hadin guiwar tsaro a tsaaninsu, wajen hada karfinsu waje guda domin tunkarar yan ta ;addan dake ikrarin jihadi suna shuka ta’annati a cikin kasshensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.