Isa ga babban shafi

Takunkumin ECOWAS ya hana Nijar biyan basussukan da ake bin ta

NIJAR – Kungiyar dake kula da basussukan kasashen dake yammacin Afirka ta sanar da cewar Jamhuriyar Nijar ta gaza biyan basussuka da kuma kudaden ruwan rancen da ta ciwo da yawansu ya kai dala miliyan 304 a cikin watanni 3 da suka gabata, sakamakon juyin mulkin soji.

Shugaban majalisar soji ta Nijar Janar Abdourahmane Tiani
Shugaban majalisar soji ta Nijar Janar Abdourahmane Tiani REUTERS - STRINGER
Talla

Kungiyar kasashen dake amfani da kudaden Cefa ta UMOA tace ayau talata, Nijar ta gaza biyan kudin da ya kai dala miliyan 4 daga cikin bashin da ake bin ta.

UMOA tace gazawa wajen biyan kudaden ya biyo bayan matakin da ta dauka akan Nijar da kuma takunkumin karya tattalin arzikin da shugabannin kungiyar ECOWAS suka kakabawa mata.

An dai dakatar da Nijar daga cikin hada hadar kudade da kasuwanci a hukumar kudade na yankin ne tun bayan kifar da gwamnatin shugaba Bazoum Mohammed.

ECOWAS ta sanya takunkumi masu tsauri a kan sojojin Nijar, ciki harda hana su amfani da kudaden ajiyarsu na kasashen ketare dake bankin shiyar, tare da barazanar amfani da karfin soji domin mayar da doka da oda a kasar.

Jamhuriyar Nijar ce kasa ta 3 da sojoji ke gudanar da mulki a Afirka ta Yamma, baya ga Mali da Burkina Faso.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.