Bakonmu a Yau
Lamido : Buhari na daukar kasa da abinda ke ciki ganima...
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:12
Tsohon gwamnan jihar Jigawa a Najeriya kuma Kusa a jamiyyar PDP mai adawa Alhaji Sule Lamido, ya ce ba wani abin mamaki a game da yadda shugaban kasar Muhammadu Buhari ke tafiyar da mulkar kasar, saboda a cewarsa shugaban na kallon kasar da kuma abin da ke ciki a matsayin ganimar nasarar da ya yi a zabe.To sai dai tsohon gwamna Lamido, ya ce ya yi imanin babu makawa Jamiyyarsu ta PDP ce za ta karbi mulkin Najeriya a zabe mai zuwa, amma da sharadin ‘yayan jam’iyyar za su hada kansu.