Yanayin da jama'a ke rayuwa a jamhuriyar Nijar biyo bayan juyin mulki a Burkina Faso
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:13
A jamhuriya Nijar, fargabar yajin aikin da ake samu a wasu kasashe ya haifar da rade radi a cikin kasar, musamman yadda ake yadawa a kan shafukan sada zumunta, kwanaki kadan bayan sojoji sun karbe mulki a makwafciya kasar ta Burkina Faso, lamarin da ake ganin zai iya yin tasiri ta fuskar zaman lafiya kasar.
Yayinda a daya geffen dakarun Jamhuriyar Nijar ke samu nasarar fatattakar mayakan kungiyar dake da’awar kafa daular musulunci a Afrika ta yamma ISWAP,mayakan da suka yi kokarin kai wani harin kwantar bauna a Chetima Wangou dake yankin Diffa dab da kogin Chadi.
Akan wannan wakilin mu Umar Sani ya tattauna da Malan Hamma Alasane, kwararre kan sha’anin sadarwa a jami’ar garin Agadas ga kuma yadda tattaunawa su ta kasance.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu