Injiniya Kelaini Muhammed kan yawan man da NNPC ke fitarwa a Najeriya
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:58
Sakamakon takaddamar da ta kaure tsakanin kamfanin man Najeriya na NNPC da Hukumar Kwastam akan yawan man da ake fitarwa kowacce rana, yanzu haka ‘yan Najeriya sun bukaci gudanar da bincike don fayyace gaskiyar al’amura.
Kamfanin NNPC yace a shirye yake ya gabatar da takardun sa ga binciken kasashen duniya, bayan zargin da shugaban kwastam ya masa cewar babu gaskiya akan alkaluman da yace ana fitarwa na mai kowacce rana.
Dangane da wannan takaddama, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon babban jami’in NNPC, Injiniya Kelaini Muhammed.
Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu