Barista Solomon Dalung kan biyan diyya ga mutanen da SARS suka zalunta
Wallafawa ranar:
Kunna - 04:19
Gwamnatin Najeriya ta biya ‘yan kasar 74 da aka tabbatar da cewar jami’an 'yan sanda, reshen masu yaki da 'yan fashi da makamai da aka rusa wato SARS sun ci zarafinsu diyyar Naira miliyan 289.
Shugabar Hukumar Kare Hakkin Bil'adama ta kasa, Dr. Salamatu Suleiman ta gabatar da kudaden ga wadannan mutane 74, inda ta bayyana cewar kafin su, an biya wasu mutane 94 da suka fuskanci irin wannan cin zarafi Naira miliyan 431.
Dangane da wannan mataki, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Barr. Solomon Dalung, tsohon minista kuma lauya mai zaman kansa a Najeriya.
Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu