Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Sada Ladan kan yadda Dangote ya mallaki kamfanin simintin Obajana dake Kogi

Wallafawa ranar:

Da alama har yanzu tsugune bata kare ba game da dambarwar tsakanin kamfanin simintin Attajirin Afrika Aliko Dangote da gwamnatin jihar Kogi dangane da hakikanin wanda ya mallakin kamfanin, bayan da a baya-bayan nan gwamnatin ta fara yunkurin kwace iko da kamfanin wanda ta yi ikirarin cewa ta mallaki wani sashe na sa, yayinda Dangote ke sake jaddada cewa shi ke da ikon dari bisa dari na kamfanin.

Katafaren kamfanin simiti na Dangote da ke Obajana a jihar Kogi
Katafaren kamfanin simiti na Dangote da ke Obajana a jihar Kogi © Daily Trust
Talla

Kamfanin simintin na Dangote ya ce tun a shekarar 2002 ne ya mallaki hannayen jarin kamfanin siminti na Obajana da ke jihar Kogi, tare da tabbatar da mallakar hannayen jarin ɗari bisa ɗari.

Rukunin Kamfanonin Dangote na martani ne ga gwamnatin jihar Kogi, wadda ta rufe kamfanin simintin bisa zargin cewa ba'abi ka'ida ba wajen mallakar hannun jarin.

Kamfanin hamshakin attajirin na Afirka Alhaji Aliko Dangote ya ce sun sauke duk wani wajibi da ke wuyansa, kama daga biyan haraji na biliyoyin naira zuwa kyautata wa al'ummomin da ke rayuwa a inda kamfanin yake.

Alhaji Sada Ladan baki Babban daraktan kula da harkokin masana'antu na kamfanin ya yi karin haske kan lamarin a zantawarsa da Ahmad Abba.

Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.