Manoman Najeriya sun koka kan shigar musu da takin zamani maras inganci
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:35
Manoma a Najeriya sun bukaci mahukunta da su kara sanya ido, domin yaki da wadanda ke shigar da takin zamani maras inganci a cikin kasar.
Alhaji Umar Ya’u Gwajo-Gwajo, daya daga cikin shugabannin kungiyar manoma a Najeriya, kuma shahrarren manomi a jihar Katsina, ya ce tabbas manoma na iya kokarinsu domin wadatar da kasar da abinci, amma duk da haka akwai bukatar gwamnati ta sanya ido domin samar da ingantaccen takin zamani a cikin kasar.
Ga dai abin da ya shaida wa Abdoulkarim Ibrahim Shikal a zantawarsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu