Sojojin Ivory Coast 46 sun koma gida bayan shafe watanni 6 tsare a Mali
Wallafawa ranar:
Kunna - 04:09
Sojojin Ivory Coast 46 sun koma gida bayan shafe tsawon watanni 6 a hannun gwamnatin sojin Mali da ta tsare su kan zargin yi wa tsaron kasarta zagon-kasa, al’amarin da ya rura wutar gabar diflomasiya tsakanin kasashen biyu.
Da fari dai gwamnatin Mali ta yanke wa sojojin hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari, amma daga bisani ta yi musu afuwa bayan masu shiga tsakani sun sasanta su.
A game da wannan batu, Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattuana da Al-Kasim Abdurrahman,mai sharhi kan al’amuran kasashen Afrika a Jamhuriyar Nijar
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu