Bakonmu a Yau
Garba Rabiu dan siyasa a Benin kan yadda 'yan adawa suka lashe kujerun Majalisa 28
Wallafawa ranar:
Jam’iyyar adawa a Jamhuriyar Benin ta lashe kujeru 28 a zaben majalisar dokokin da aka yi a kasar a karshe makon da ya gabata, kamar yadda sakamakon farko da hukumar zaben kasar ta fitar a yau Laraba. Wannan lamarin ya maida jam’iyyar adawar majalisar mai kujeru 109 bayan da ta shafe shekaru 4 ba a damawa da ita. Adoulaye Issa ya samu tattaunawa da Garba Rabiu dan siyasa kuma wakili a majalisar da’irar Lokossa na kasar ta Benin.