Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Kasimu Abdo Saulawa-Tasirin matsaloli yayin zaben Shugaban tarrayar Najeriya

Wallafawa ranar:

A Najeriya, yayin da ake ci gaba da kada kuri’u domin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya a wannan asabar, rahotanni na nuni da cewa an samu matsaloli da dama da suka hada da na’urar BVAS da ke tantance masu kada kuri’a, da rashin alamun wasu jam’iyyu (wato logo) a kan takardun zabe. An fara kada kuri’un ne a makare saboda rashin isowar jami’an zabe a kan lokaci, yayin da aka samu hare-haren kan jami’an zabe a wasu jihohi,kamar dai yada zaku ji a wannan tattaunawa tsakanin Kasimu Abdo Saulawa, da ke bin diddigin yadda wannan zabe ke gudana,da Abdoulkarim Ibrahim Shikkal.

Lokacin da jami'an zabe suka halarci rumfar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya kada kuri'arsa a birnin Lagos. (2023/02/25)
Lokacin da jami'an zabe suka halarci rumfar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya kada kuri'arsa a birnin Lagos. (2023/02/25) AP - Ben Curtis
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.