Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Bashir Nuhu Mabai kan dagen zaben Najeriya da INEC ta yi

Wallafawa ranar:

A ranar Laraba ne hukumar zaben Najeriya INEC ta sanar da cewa an dage zaben gwamnoni da na 'yan majalisun jihohi da aka shirya gudanarwa ranar 11 ga watan Maris.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu REUTERS - REUTERS TV
Talla

INEC ta ce yanzu haka an tsawaita lokacin zaben zuwa ranar 18 ga watan na Maris, sakamakon aikin da za ta yi na sake fasalta na'urar tantance masu kada kuri'a ta BVAS, da kotu a kasar ta bayar da umarnin yin hakan.

A cewar INEC ba za ta iya aikin sake fasalta na'urar ta BVAS a cikin kwanaki biyu ba, don haka tana bukatar isasshen lokaci.

Shiga alamar sauti, domin jin tattaunawar da Bashir Ibrahim Idris ya yi da Bashir Nuhu Mabai, masanin siyasa a jami'ar tarayya da ke jihar Katsinan Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.