Boulama Alhaji Gori kan halin da bakin haure ke ciki a iyakar Aljeriya
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:32
Kungiyar agaji ta MSF, ta bukaci kasashe mambobin kungiyar ECOWAS ko CEDEAO, da su gaggauta kwaso dubban 'yan kasarsu, wadanda ke makale a lardin Assamaka da ke kan iyakar Aljeriya da Jamhuriyar Nijar.
Bakin, wadanda yawan su ya kai kusan dubu biyar, sun samu kawunansu a cikin mawuyacin hali, bayan Aljeriya ta taso keyar su zuwa kasar Nijar.
Game da halin da bakin hauren ke ciki ne, Umar Sani ya tattauna da Boulama Alhaji Gori, mataimakin shugaban kula da ayyukan kungiyar MSF a yankin Afirka ta Yamma.
Shiga alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu