Dakta Ahmad Salisu kan gargadin gwamnatin Najeriya ga Peter Obi
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:58
Gwamnatin Najeriya ta gargadi dan takarar shugabancin kasar a jam’iyyar Labour Party wanda ya sha kaye a zaben da ya gabata Peter Obi, da ya yi taka-tsantsa a game da kalaman da yake furta dangane da sakamakon wannan zabe, wadanda a cewar gwamnati ka iya haddasa boren al’umma.
A lokacin wata ganawa da manema labarai a birnin Washington na kasar Amurka, ministan yada labaran Najeriya Alhaji Lai Muhammad, ya ce barazanar da Obi ya yi idan har aka rantsar da zababben shugaban kasar, kalamai ne da a gaban doka za a iya fassara su a matsayin cin amanar kasa.
Kan haka ne Khamis Saleh ya tattauna da Dakta Ahmad Salisu Garba, masanin harkokin shari’a a kasar.
Shiga alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu