Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

INEC ta ce ta shirya gudanar da zaben cike gibi a Najeriya

Wallafawa ranar:

Hukumar zaben Najeriya ta ce, ta shirya gudanar da zabukan cike gibi da suka rage, kama daga gwamnoni da 'yan majalisun tarayya da kuma na jihohi.

Shugaban hukumar INEC farfesa Mahmud Yakubu kenan, lokacin da yake karbar sakamakon jihohi na zaben shugabancin kasar da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.
Shugaban hukumar INEC farfesa Mahmud Yakubu kenan, lokacin da yake karbar sakamakon jihohi na zaben shugabancin kasar da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023. AP - Ben Curtis
Talla

A cewar hukumar ta INEC, tuni aka mika kayayyakin zabe da ake bukata a yankunan da zabukan suka shafa da ke fadin jihohin kasar, gabanin zaben da za a yi ranar Asabar.

Daga cikin zabukan da ssuka fi daukar hankali, akwai na gwamnan jihar Adamawa, da ake fafatawa tsakanin Sanata Aisha Dahiru Binani, daga jam’iyyar APC mai mulkin kasar, da kuma gwamna mai ci wato Ahmadu Fintiri na babbar jam’iyyar adawa ta PDP.

Dangane da wannan shirin da hukumar INEC ta ce ta yi, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Zainab Aminu Abubakar, jami’ar hulda da jama’a ta hukumar a Najeriya.

Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.