Samaila Mohammed kan yadda matsalar bankuna ta shafi 'yan Najeriya
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:53
Rahotanni daga Najeriya sun ce akalla kashi 40 na mutanen kasar da suka aike da sakwannin kudade ta waya daga cikin kashi 100 basu samu kudaden na su ba, kuma aiken bai kai ga mutanen da aka turawa ba.
Alkaluma sun nuna cewar yayin da aka samu karuwar aikewa da sakwannin kudaden ta wayoyin hannu, jama’a na shan wahala wajen samun kudadensu da suka makale a bankuna sakamakon irin wadannan sakwanni.
Babban Bankin Najeriya a shekarar 2020 ya bai wa bankuna umurnin mayar wa jama’a kudadensu a cikin kasa da makwanni 2 idan an fuskanci irin wannan matsala.
Dangane da wannan matsala, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin tattalin arziki, Samaila Mohammed.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu