Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Tattaunawa da Hauwa Mustapha Babura kan sakin daliban kwalejin Yawuri a Kebbi

Wallafawa ranar:

Rahotanni daga Najeriya sun ce anyi nasarar kubutar da sauran dalibai ‘yan mata guda 3 da suka rage a hannun ‘yan ta’addan da suka sace su a Kwalejin Yawuri ta jihar Kebbi cikin shekarar 2021.

Iyayen wasu dalibai da aka yi nasarar cetowa daga hannun 'yan bindiga.
Iyayen wasu dalibai da aka yi nasarar cetowa daga hannun 'yan bindiga. REUTERS - AFOLABI SOTUNDE
Talla

Shugaban kungiyar iyayen daliban da aka sace, Salim Ka’oje ya sanar da sakin daliban guda 3 a ranar lahadin da ta gabata, bayan an biya kudin fansa.

Wadanda aka sake sun hada da Aliya Abubakar da Esther Sunday da kuma Elizabeth Nwafor.

Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da daya daga cikin mutanen da suka yi ta fafutukar ganin na kubutar da daliban Hauwa Mustapha Babura, mazauniyar kasar Amurka, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.

Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar......

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.