Bakonmu a Yau
Chehou Azizou a kan yarjejeniyar gwamnatin Nijar da kasashen waje game da bakin haure
Wallafawa ranar:
Kungiyoyin fararen hula a Jamhuriyar Nijar sun bukaci Karin haske a kan yarjeniyoyin da gwamnatin kasar ke kullawa da kasashen ketare a kan hana baki daga yankin Sahel ratsawa ta kasar suna tafiya Turai. A karkashin wannan yarjejeniyar ce ake kwashe bakin yan Afirka ta Yamma ake jibgewa a cikin kasar. Dangane da wannan bukata, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Shehu Azizu, mai kare hakkin baki a Agadez.