Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Hassan Gimba a kan wa'adin mika mulki da sojojin Nijar suka diba

Wallafawa ranar:

A daidai lokacin da kasashen duniya ke kokarin samar da mafita ga rikicin siyasar da ake fama da shi a Jamhuriyar Nijar, jagoran sojojin da suka kwaci mulki a kasar Janar Abdourahman Tchiani ya ce yana fatan shimfida tsarin rikon kwarya da bai gaza shekaru uku ba. 

Taswirar wani sashi na Jamhuriyar Nijar
Taswirar wani sashi na Jamhuriyar Nijar © RFI
Talla

 

Janar Tchiani ya sanar da hakan ne a daren asabar da ta gabata, jim kadan bayan ganawa da tawagar kungiyar Ecowas da kuma ta MDD a birnin Yamai, inda ya kara da cewa zai shirya wani babban taro domin jin ra’ayoyin kowane banagare na al’ummar kasar a cikin wata daya. 

Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Alhaji Hassan Gimba, marubuci kuma mai bin diddigin siyasar kasashen Afirka, domin jin yadda yadda ya kamata duniya ta tunkari wannan batu na Jamhuriyar Nijar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.