Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Masu satar danyen mai na haddasawa Najeriya asarar dala miliyan 4 kowacce rana

Wallafawa ranar:

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa, kasar na tafka asarar kimanin Dala miliyan hudu a kowacce rana sakamakon yadda wasu tsageru ke satar gangunan danyen man fetur dubu 400 a kullum a yankin Niger Delta, lamarin da ta ce, na kara ta’azzara matsin tattalin arzikin kasar. 

Gwamnatin Najeriya ta ce a kowacce rana kasar na tafka asarar fiye da dala miliyan 4 saboda masu satar danyen man fetur.
Gwamnatin Najeriya ta ce a kowacce rana kasar na tafka asarar fiye da dala miliyan 4 saboda masu satar danyen man fetur. REUTERS/Athit Perawongmetha(T
Talla

A karshen mako ne, wata babbar tawagar kusoshin gwamnati karkashin jagorancin Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Lamurran Tsaro, Nuhu Ribadu ta ziyarci yankin na Niger Delta tare da yin nazari kan yadda za a magance satar danyen man. 

A kan haka ne, Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna da Alh. Mukhtar Hussain, masanin tattalin arziki a Najeriya. 

Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakkiyar hirar.......

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.