Bakonmu a Yau
Wa'adin da shugaba Tinibu ya bada na karbo kudin gwamnati daga hannun manoma ya cika
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:40
Yau litanin 18 ga watan satumba 2023, wa’adin da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya baiwa jami’an tsaro, domin kwato sama da naira biliyan 500 daga cikin kudaden rancen da aka bai wa manoma a karkashin babban bankin Najeriya na ‘Anchor borrower’ ke cika. Domin sanin inda aka kwana da kuma halin da ake ciki, mun tintibi Sakataren Tsare tsare na kungiyar manoman Najeriya ta AFAN, Alhaji Muhammadu Magaji, kuma ga tsokacin da yayi akai.