Malam Zubairu Sani kan dakatar da alkalan wasa da hukumar NFF ta yi
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:27
Hukumar da ke kula da kwallon kafa a Najeriya ta NFF ta dakatar da wasu alkalan wasan da ke busa gasar firimiya league su 14 daga aiki, saboda abinda ta kira kura kuran da suka tafka wajen gudanar da alkalancin wasannin da ke gudana a wannan kaka. Irin wadannan kura kurai na daga cikin dalilan da suka saka hukumar kwallon kafa ta Afirka wato CAF kan tsallake alkalan wasan Najeriya lokacin zabo wadanda za su busa wasannin Afirka.
Ko gasar da za a gudanar a Abidjan shekara mai zuwa, babu alkalin wasa koda guda daga Najeriya. A kan wannan ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shugaban alkalan wasan Najeriya, Malam Zubairu Sani.
Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar tasu....
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu