Shirin a wannan mako ya mayar da hankali ne kan gudunmawar sabuwar fasahar nan ta Artificial Intelligence ko kuma AI wadda ke bayar da damar sanyawa na’urori basirar dan adam, ko kuma baiwa na’urorin damar yin ayyukan da dana dam ke yi a bangarori na rayuwa, fasahar da ake ganin za ta taimaka matuka ga bangaren lafiya.
Tun gabanin bunkasar fasahar ta AI, a shekarun 1960 zuwa 1970 aka fara amfani da makamanciyar fasahar karkashin shirin Dendral wanda ya bayar da damar kirkirar na’urar MYCIN da ke lakantar cutukan jikin dan adam da kuma bayar da magunguna ba tare da sa hannun kwararru ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu