Shirin Rayuwata na wannan rana ya yi nazari ne kan halin kuncin da zaurawa ke tsintar kansu a ciki bayan rabuwa da mazajensu, inda kacokan suka daukar nauyin kansu da na 'ya'yansu ba tare da samun wani agaji daga wajen iyayensu ko kuma al'umma ba.
Sauran kashi-kashi
-
Yadda matan Nijar suka dage wajen neman kuɗi
Mata a Jamhuriyar Nijar sun dage sosai wajen neman na kansu a maimakon ci gaba da dogara kan mazajensu, yayin da wasu ƙungiyoyi daban daban suka yunkuro domin tallafa wa matan da abubuwan gudanar da sana'o'insu.31/05/202410:00 -
Ra'ayoyin masu sauraren shirin Rayuwata
Shirin Rayuwata na wannan rana ya mayar da hankali ne kan ra'ayoyin masu sauraren sa daga sassan duniya game da shirye-shiryen da suka gabata a wannan makon.30/05/202410:00 -
Bikin Ranar Matan Jamhuriyar Nijar
Shirin Rayuwata na wannan rana ya tattauna ne kan bikin Ranar Matan Jamhuriyar Nijar da ake gudanarwa a duk ranar 13 ga watan Mayu. Ranar ta samo asali tun shekarar 1991, lokacin da matan Yamai suka gudanar da wata zanga-zanga domin kwato ƴancin mata a siyasa.24/05/202410:00 -
Ra'ayoyin Masu Sauraren Shirin Rayuwata
Shirin Rayuwata na wannan rana ya saurari mabanbantan ra'ayoyin jama'a kan shirye-shiryen da aka gudanar a wannan makon.23/05/202410:00 -
Yadda ake tsangwamar matan da suka yi zaman gida yari a Nijar
Shirin Rayuwata na wannan rana ya yi nazari kan yadda jama'ar ke tsangwamar matan da suka taba yin zaman gidan yari a Jamhuriyar Nijar. Matan sun bayyana irin kalubalen da suke fuskanta, suna masu cewa, akan yi musu zinɗe da nuna kyama, yayin da wasu mazan ke cewa, ba za su yarda su yi hulɗa da ire ire waɗannan matan ba.22/05/202410:00