Isa ga babban shafi
Rayuwata

Yadda wasu mata masu juna biyu ke sauya halayyarsu

Wallafawa ranar:

Shirin na yau ya tabo batun yadda wasu mata masu juna biyu kan sauya halayen su, musamman ta fuskar zamantakewa tsakanin su da mazajensu.

Ana danganta sauyawar halayayen masu juna biyu da irin halin da suke tsintar kan su
Ana danganta sauyawar halayayen masu juna biyu da irin halin da suke tsintar kan su Reuters/Carlos Barria
Talla

Sau da dama mata masu dauke da juna biyu kan fuskanci kalubale na laulayi, wanda shine abin tashin hankali ga wasu matan baya ga ita kanta nakudar haihuwa.

Akwai ‘yan rashin lafiya da wasu mata kan fuskanta tsawon lokacin da suke dauke da juna biyun kafin haihuwa.

Bugu da kari akwai wasu abubuwa na daban da suka zama jiki ga kowacce mace mai ciki, wadanda suka hada da kwadayi, rashin cin abinci ko kuma cin abinci fiye da kima, amma wani babban abu da ke daukar hankali shine ta yadda lallurar juna biyu kan sa wasu matan nuna kiyayya ga mazajensu har sai lokacin da suka sauke nauyin dake tattare da su.

Latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin da Zainab ibrahim ta shirya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.