Shirin Rayuwata na wannan rana ya yi nazari ne kan matsalar nan ta cin zarafin da magidanta ke yi wa matansu na aure, lamarin da har yanzu ke ci gaba da zama ruwan dare game duniya a kasashen Afrika.
Shirin ya yada zango a Ghana, inda wannan matsalar ta cin zarafin matan aure ta yi kamari kamar yadda binciken Hukumar 'Yan Sandan Kasar ya nuna.
Shirin ya zanta da wata baiwar Allah mai suna Habiba Khalid wadda mijinta ya yi mata dukan kawo-wuka bayan ya zarge ta da zantawa ta wayar tarho da wani mutun wanda ba muharraminta ba ne.
Ku latsa alamar sauti domin sauuraren cikakken shirin tare da Zainab Ibrahim
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu