Dalilin da ya sa mazan Najeriya ke kyamar matan da ke aiki a Otal
Wallafawa ranar:
Kunna - 10:00
Shirin ya mayar da hankali kan yadda ake tsangwamar matan da ke aiki a gidajen otal-otal, musamman a Arewacin Najeriya, inda ake musu kallon masu zaman kansu ko kuma masu yawon dandi.
A duk lokacin da aka ce mace na aiki a Otal, to kuwa kusan kabilu da dama suna masa kallon aiki mai cike da abun kyama, musamman ga mata, kasancewar mutane masu halayya daban-daban kan kai ziyara ire-iren wadannan wurare.
Shirin ya tattauna da wasu daga cikin matan da suke aiki a Otal, duk da kalubalen da suka fuskanta daga wurin iyayensu kafin su fara aikin, da kuma yadda masana ke kallon wannan al'amari.
Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin, tare da Zainab Ibrahim.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu